IQNA

Mutane Miliyan 3 A Taron Tuwairij A Karbala Moqaddasa

19:25 - October 24, 2015
Lambar Labari: 3393133
Bangaren kasa da kasa, cibiyar hubbaren Imam Hussain (AS) ta cewa mutane miliyan 3 ne suka halarci taron Tuwairij a karbala a yau.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga Saumaria News cewa, kimanin mutane miliyan 3 ne suka gudanar da sassarfar da aka saba gudanarwa  atsakanin hubbarori biyu masu tsarki a birnin karbala mai alfarma a yau.
Rahotanni daga kasashe daban-daban na duniyar Shi’a  suna nuni da cewa miliyoyin mabiya Ahlulbaiti (a.s) da ma sauran ‘yantattun al’ummomi na duniya suna shirin gudanar da jerin gwano da sauran bukukuwan ranar Ashura, wato ranar goma ga watan Muharram don tunawa da ranar shahadar Imam Husain (a.s) tare da mabiyansa a Karbala.
A kasar Iraki, rahotanni na nuni da cewa miliyoyin al’ummar musulmi ne daga ciki da wajen kasar suke ne suke ta tururuwa zuwa garin na Karbala don girmama wannan rana cikin tsauraran matakan tsaro don kare lafiyar masu ziyarar daga hare-haren ‘yan ta’adda.
A nan jamhuriyar muslunci ma miliyoyin al’ummar kasar suna ci gaba da gudanar da tarurrukan da jerin gwanon Ashurar a dukkanin garuruwan kasar bayan sun shafe daren jiya suna gudanar da irin wadannan tarurruka.
A kasar ma miliyoyin mabiya tafarkin Imam Hussain  (a.s) ne suke ci gaba da gudanar da irin wadannan jerin gwano a yankin Dhahiya da ke kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar inda a ke sa ran shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah zai gabatar da jawabi a wajen taron.
A jiya ma miliyoyin mutane a ciki da wajen kasar Iraki suna ci gaba kwarara zuwa birnin Karbala da ke tsakiyar Iraki domin gudanar da juyayin ranar Tasu’a, ranar da rundunar Ibnu Ziyad suka killace jikan Manzon Allah Imam Husaini da iyalansa gami da sahabbansa a wajen da babu ruwa a shekara ta 61 bayan hijira.
A halin yanzu haka miliyoyin mutane daga cikin kasar Iraki gami da sassa daban daban na duniya suna ci gaba da tururruwa zuwa birnin Karbala domin gudanar da juyayin ranar Tasu’a a yau Juma’a gami da alhinin ranar Ashura a gobe Asabar a karkashin tsauraran matakan tsaro.
A gefe guda kuma mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} wato ‘yan shi’a a sassa daban daban na duniya suna ci gaba da gudanar da juyayin ranar .

 

3393114

Abubuwan Da Ya Shafa: ashura
captcha