IQNA

An Bude Baje Kolin Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Qatar

22:33 - November 09, 2015
Lambar Labari: 3446388
Bangaren kasa da kasa, an bude baje kolin kur’ani mai tsarki da aka saka kwafin kur’anai 60 da suke da alaka da lokuta mabanbanta a kasar Qatar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-rayah ta Qatar cewa, Hamad Bin Abdulaziz Alkawadiri minister mai kula da harkokin aladu na kasar ya halarci wurin bude taron baje kolin a cibiyar yada aladu ta Izdan Mall da ke kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa an bude baje kolin kur’ani mai tsarki ne wanda aka saka taken Mushafin Rihlah tare da baje kwafin kur’anai 60 da suke da alaka da lokuta mabanbanta da ya hada har da lokutan bayan ma’aiki (SAW)

Ana gudanar da wannan baje koli ne a wannan cibiyar yada al’adu ta Izdan Mall wadda ke da fadin mita murabbai 300 da ke samun halartar jama’a  akowane.

Za a ci gaba da gudanar da wannan baje koli har zuwa kusan makonni biyu a nan gaba, domin bayar da dama ga masu halartar wurin da suke son ganin wadannan kwafin kur’anai da aka kawo a wurin.

Daga cikin wadannan kur’anai a kwai na lokuta daban-daban a cikin tarihin addinin mulsunci, da suka hada da wadanda ska haura shekaru dubu daya da wani abu, da kuma wasu na darruwan shekaru.

3446036

Abubuwan Da Ya Shafa: qatar
captcha