IQNA

Wani Yaro Dan Shekaru 9 Daga Somalia Shi Ne Mafi Karancin Shekaru A Gasar Kur’ani Ta Saudiyya

22:34 - November 09, 2015
Lambar Labari: 3446389
Bangaren kasa da kasa, Abdussamad bin Umar Muhammad dan kasar Somalia shi ne mafi karancin shekaru a gasar kur’ani ta kasa da kasa a Saudiyyah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sauress.com cewa,  Abdussamad bin Umar Muhammad dan shekaru 9 da haihuwa, daga kasar Somalia shi ne mafi karancin shekaru a gasar kur’ani ta kasa da kasa a Saudiyyah da ake gudanarwa.

Shi dai mahardacin dukkanin kur’ani mai tsarki ne duk kuwa da karancin shekarunsa, wanda ya halarci tarukan gasar kur’ani a cikin kasar ta Somalia kuma yana nuna kwazo matuka.

Abdussamad bin Umar Muhammad dangane da wannan gasa ta kasar Saudiyyah ya bayyana cewa, hakika ya ji dadin halartar wannan gasa, domin kuwa ko ba komai dai a halin yanzu gas hi ga kma dakin Ka’abah mai tsarki, kuma wannan shi ne karon farko da yake halartar gasa a waje.

Wanda yake kula da shi kuma y aba shi tarbiyar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ya bayyana cewa, a kowace rana Abdussamad yana karanta juzui 10 daga kur’ani mai tsarki.

Ya hakarci gasar kur’ani a sassa daban-daban na Somalia kuma  akowane lokaci yana zuwa matsayi na daya ne.

Wannan dais hi ne karo 37 da ake gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Saudiyya  amtaki na kasa da kasa, wadda aka fara 16 ga watan Aban a karkashin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar, tare da sa idon sarkin kasar.

Mahalarta 124 ne suka zo gasar daga kasashe 66 na duniya.

3444804

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya
captcha