IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ba Kungiyar Ta’addanci Ba Ce

16:47 - November 16, 2015
Lambar Labari: 3453385
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Mikhael Bogdanov ya bayyana cewa kungiyar Hizbullah ba kungiyar ta’addanci ba ce.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na SAMA cewa, a wtattaunawar da mataimakin ministan harkokin wajen Rasha ya yi da Interfox ya bayyana cewa, kungiyar Hizbullah ba ta ta’addanci ba ce.

Ya ce muna da kyayyawar alaka da da kungiyar Hizbullah kuma har yanzu wannan alaka tana tafiya ba tare da wata matsala ba, kuma a bin muka sani shi ne kunya ce ta ‘yan kasa.

Mataimkin ministan harkokin wajen na Rasha ya kara da cewa tun da aka kafa kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon har zuwa yau ba a taba jin wani aikin ta’addanci da kungiyar Hizbullah ta yi a cikin kasar Lebanon ko wani wuri ba.

Malamin Ahlu Sunna Ya Yabi Jawabin Sayyid Hassan Nasrullah

Daya daga cikin manyan malaman ahlu sunna a Lebanin Sheikh Hussam Al-ilani ya bayyana gasuwarsa matuka dangane da jawaban da jagoran kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah damnagge da abin da ya faru.

Malamin ya ce ko shkaku abin da Sayyid Hassan nasrullah ya fada dangane da abubun da suka faru ko kuma suke faruwa a yankin shi ne hakikanin gaskiyar lamari, domin kuwa yan ta’adda barazana ne ga kowa.

Ya kara da cewa ya zama wajibi a kan malamai na addini da su safke nauyin da ya rataya a kansu na fadakar da jama’a kan hakinanin addini da kuma abin da yake koyarwa, domin kuwa rashin sanin addini shi ne bababn ummul haba’sin fadawa cikin wannan balai da mutane suke yi da sunan suna yin addini.

Daga karshe yay i kira ga malamai da su yi koyi da mutane irin su Sayyid Hassan Nasrullah, wanda ya sadaukantar da rayuwarsa domin kare addininsa da al’ummarsa.

3453135

Abubuwan Da Ya Shafa: rasha
captcha