IQNA

An kashe Wanda Ya Shirya Harin Paris / Daesh ta Yi Barazanar Kashe Malaman Azhar

23:19 - November 20, 2015
Lambar Labari: 3454810
Bangaren kasa da kasa, mahkunta a kasar Faransa sun tabbatar da mutuwar mutumin da ya shirya harin ta’addancin birnin Paris.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, majiyoyin tsaro a Faransa sun an kashe Abdulhamid Aba’ud, mutumin da ya shrya kai hare-haren birnin Paris a ranar Juma’a da ta gabata, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Jmai’an tsaron na Faransa sun ce sun kai samame ne a ranar laraba da ta gabata a yankin San Doni da ke arewacin birnin.

Harin Paris dai ya yi sanadiyyar mutane 129, tare da jikkatar wasu fiye da dari uku.

Yan Ta’addan Daesh Sun Yi Barazanar Kashe Malaman Azahar

Kungiyar daesh ta yi barazanar kashe malaman cibiyar Azahar sakamakon rashin amincewa da ayyukan kungiyar da kuma fatawowin da suke bayarwa na haramta ayyukanta.

Jarid sun ruwaito cewa, sun nakalto daga wasu manyan jami’ai a bangaren leken asiri a kasar cewza jami’an tsaro sun kashe mutumin amma ba su karin haske kan lamarin ba, sai sun bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, bayan kashe wasu mutane biyu a jiya arewacin birnin da aka bayyana cewa suna da alaka kai tsaye da hare-haren.



Abu Muha,,ad Almisri yana daga cikin manyan kwanadojin Daesh shi ne kuma ya yi barazana a kan malaman Azahar da kisa bayan fatawar da suka bayar bayan harin, wanda ya shirya harin dan asalin kasar magrib ne, amma yana takardun zama dan kasa na kasar baljika.



Kuma da dama daga cikin wadanda suka san shi sun bayyana cewa sun san shi a matsayin gawurtaccen barawo ne, amma kwatsam kuma sai ga shi ya bayyana a matsayin daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Daesh,  inda ake lissafa shi a matsayin daya daga cikin jagororin kungiyar.



3454650

Abubuwan Da Ya Shafa: France
captcha