IQNA

Ta Yaya Aka Share Sunan Dan Shi’a Da Ya Fi Kudi Daga Tarihi

21:04 - November 23, 2015
Lambar Labari: 3456298
Bangaren kasa da kasa, shekaru 15 da suka gabata ne a tsakiyar watan Nuwamban shekara ta 2000 aka share sunan mutumin da kudin shigarsa na shekara dala biliyan 60 ne daga tarihi saboda ya zabe bin Ahlul bait (AS)


Kamfanin dillancin labaran Iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, an haifi Edward Anily ne a ranar 9 ga watan Ynin shekara ta 1954 a birnin New York na kasar Amurka.





Ya yi karatu mai zurfi a bangarori daban-daban da suka hada da lissafi da kuma falsafa, kamar yadda kuma ya kasance mutum ne mai matukar bincke kan lamurra da suka danganci a addinai.

Sanata Anily shi ne mahaifin Edward, wanda kuma mutum ne da ya shahara ta fuskar siyasa da kudi a kasar Italiya, domin kuwa yana da manyan kamfanoni da suka hada da kamfanin kera motoci na FIAT da kuma wasu sanannu wurare da kafofin yada labarai a kasar, gami da kungiyar kwallo ta Juventus.

Kos hakka babu sakamakon bincike da ya yi kan kur’ani mai tsarki, hakan ya sanya shi bin kadun addinin muslunci, inda daga karshe ya ziyarci jamhuriyar Mslunci ta Iran, inda ya gana da marigayi Imam Khomeni (RA) bayan juyin jya hali.

Wani abu wanda ya daukar masa hankali kuma ya yi masa tasiri yadda ya ga rayuwar Imam wanda hakan ya sanya shi tunanin cewa lallai addinin da mutumin nan yake a kansa shi ne gaskiya, wanda kuma bisa amsoshin da ya samu na daga tambayoyin da yake da su a kan addini, ya karbi addinin musulunci bisa koyarwar iyakan gidan manzo.





Wannan lamari ya tasiri a cikin zuciyarsa inda ya yi watsio da dukkanin abun duniya ya sanya son addini da Ahlul bait (AS) a gaba tare da taimakon abokinsa Hussain Abdullahi dan kasar Iran, wanda kuma alakarsa da Iam da kuma jamhuriyar muslunci ta Iran, hakan ya sanya wasu yahudawan sahyuniya da suke da tasiria  kasar Italiya daukar matakin ganin sun kawar da shi daga duniya.





Daga karshe an hada baki da abokinsa na kusa da shi aka yi masa kisan gilla, wanda hakan ya yi sanadiyyar yin shahadarsa, an kuma tsinci gawarsa ne a yashe bayan an kashe, amma daga bisani a cikin shekara ta 2001 ta hanyar wasu daga cikin abokansa an gane cewa an kashe shi tare da hadin baki da yahudawa ‘yan mafia na kasar ta Italiya.

3453528

Abubuwan Da Ya Shafa: italia
captcha