Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na IINA cewa, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkokin musulmi da sauran bakin da suke zaune a kasar Faransa ya bayyana damuwarsa dangane da yiyuwar bullar siyasar cutar da musulmin kasar Faransan da takura musu biyo bayan harin da aka kai babban birnin Paris.
Kafafen yada labarai sun ce daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkokin musulmin da sauran baki yana bayyana damuwarsa dangane da yiyuwar fara takurawa musulmi da cutar da su saboda wannan harin da aka kai.
Wanda ya kara da cewa ‘yan kungiyar ta su sun nuna damuwarsu ainun dangane da wannan hari na ta’addanci da ya faru, to amma duk da haka ya bayyana damuwar kan yiyuwar cutar da musulmi babu gaira babu sabar.
Ita dai gwamnatin kasar Faransan dai ta bayyana cewar za ta dau matakan nuna rashin sani ko sabo wajen mayar da martani ga wannan harin, lamarin da ke kara sanya tsoro dangane da irin matakan da za ta dauka kan musulmin kasar .
Sakamakon ci gaba da zaman dar-dar din da ake yi a kasar Faransa, ministan cikin gidan kasar ya ba wa jami’an jihohi da kananan hukumomi na kasar gaba daya umurnin suna iya sanya dokar ta baci a matsayin matakan tsaron hana sake faruwar harin da aka kai kasar.
Ministan harkokin wajen ya bayyana hakan cikin wani jawabi da yayi wa al’ummar kasar inda ya ce za a dau wasu sabbain matakan tsaron da suka hada da kara jami’an tsaro da dai sauransu.
A bangare guda gwamnatin Faransan ta kebe kwanaki uku na zaman makoki domin juyayin mutanen da suka mutu da wadanda suka sami raunuka a yayin wannan hari.
3456450