Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabah Veto cewa, fadar shugaban kasa a Tunisia ta sanar da cewa ISIS ke da alhakin kai harin birnin Tunis.
Shugaban kasar Tunusiya ya sanya dokar ta bace na tsahon kwanaki talatin sakamakon wani harin ta’addanci da aka kaiwa jami’an tsaron fadar shugaban kasar a jiya Talata Bayan kai harin, shugaban kasar Tunusiya ya yiwa ‘yan kasar jawabi, inda yayi alawadai da ta’addancin , sannan ya ce daga karfe 9 na daren yau, an tsakaita duk wani fice da huce har zuwa safiyar Alkhamis.
Ya kara da cewa kasar sa ta shiga cikin yanakin yaki da ‘yan ta’adda kuma duk wasu makamai da jami’an tsaron kasar ke bukata zai tanadar masu da shi domin yaki da ‘yan ta’addar.
Wata majiya ta kusa da shugaban kasar ta sanar da cewa jami’an tsaro ashirin ne suka rasu sakamakon bom din da ya tashi da bus din dake dauke da jami’an tsaron fadar shugaban kasa a jiya talata.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne dai yan ta’adda suka kai wani hari kan masu yawon shakatawa a kasar, wanda ya kashe mutane 38, daga cikinsu kusan 20 masu yawon shakartawa ne kasashen ketare.
Daesh ta sanar da alhakin kai wannan hari jim kadana bayan kai sa.