Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reuters Arabic cewa, Pop Francis a lokacin da yake ganawa da jagororin addinai 25 yau a birnin Nairobi na kasar Kenya ya bayyana cewa, an ayin amfani da sunan addini ne wajen ruda matasa da kuma saka tattauran da kan kai su ga ta’addanci.
Francis y ace batun tattanawa a tsakanin mabiya addinai a nahiyar Afirka ba abu ne na zabi ba, wajibi ne yin hakan.
Ya ce babu yadda za a yi a kare ayyukan ta’addanci da sunan ubangiji.
A nasa bangaren Abdulgafir Bu Sa’idi shugaban majalisar mabiya addinin muslunci a kasar ta kenya ya bayyana cewa, kasantuwarmu muna Imani da ubangiji guda daya, kuma muna rayuwa adunbiya daya, dole ne mu karbi juna mu zauna lafiya.
Abin tuni a nan shi ne bayan kasar Kenya, Pop zai kama hanaya zuwa kasar Uganda inda zai gana da yan kasar Afirka ta tsakiya da ke fama da tashin hankali.
3457317