IQNA

Fiye Da Masu Ziyarar Arba’in Miliyan Biyu Ne Suka Isa Iraki

23:12 - November 28, 2015
Lambar Labari: 3457977
Bangaren kasa da kasa, fiye da mutane miliyan biyu ne da suka hada da larabawa da Iraniyawa suka isa kasar Iraki a halin yanzu domin halartar taron arbain.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, Sami Sudani babban jami’I mai kula da harkokin shige da fice a kan iyakokin kasar Iraki ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu fiye da mutane miliyan biyu ne suka isa kasar, kuma a cewarsa sun sheda wa Iran cewa za su iya kara karbar wasu masu ziyara miliyan biyu.

Miliyoyin mutane daga cikin masoya Ahlul Bait (AS) daga koin cikin fadin duniya ne suke isa kasar Iraki domin halartar taron arbain na Imam Hussain (AS) a ciki da wajen kasar ta Iraki zuwa Karbala, musamman ma daga Iran.

3457956

Abubuwan Da Ya Shafa: karbala
captcha