Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 24.com cewa, a cikin wani sako ma’aikatar harkokin wajen kasar Switzerland ta bukaci ma’aikatar addinai a Masar da ta buga kur’anai da aka tarjama acikin harsunan Jamusanci, Italiyanci da Faransanci harsunan da aka fi amfani da su a kasar.
Baynai ya ci gaba da cewa bababr manufar hakan it ace yada al’ur’anania tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba a kasar domin su san koyawar muslunci kan cewa ba ta ta’addanci ba ce.
Wannan mataki dai ya zo sakamamon abubuwan da suke ta faruwa a halin yanzu a cikin kasashen nahiyar turai na nuna kyama ga musulmi kan batun ta’addanci, inda wasu kan fake da sunan addinin muslnci wajen aikata ta’addanci.
Muhammad Mukhtar Juma ministan ma’’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ya bayyana cewa, tuni ya bayar da umarni domin a gudanar da bincike kan wannan bukata ta Switzerland, domin sanin abin da za a yi kan lamarin.
3458345