Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfurat News cewa, a cikin bayanin da ta fitar majalisar dokokin Karbala ta bayyana cewa an gudanar da tarukan arbaeen na wannan shekara cikin lumana ba tare da wata matasala ba, kuma fiye da masu ziyara miliyan 5 ne suka halarci tarukan Arbaeen na wannan shekara daga sauran kasashen duniya daban-daban.
Alfurat News ta ce ma’aikatar kula da harkokin al’adu ta kasar Iraki ta bukaci da a saka wannan taro wanda shi ne mafi girma aduniya a cikin manyan taruka na kundin UNESCO.
Shi ma a nasa bangaren firaministan Iraki Haidar Ibadi ya ce shirin ya gudana acikin nasara, duk da cewa cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan manyan kafafen watsa labaran duniya sun ki ba wa gagarumin taro da jerin gwano na ranar arba’in din muhimmancin da ya kamata a ce an ba shi, to amma irin gagarumar fitowar da al’umma suka yi sai da ya sanya jaridar nan ta Amurka ta bayyana taron na arba’in a matsayin ‘taron addini mafi girma na duniya’ kana ta ci gaba da cewa: mutanen da suka halarci taron arba’in din Imam Husain sun ninninka wadanda suke halartar taron haji.
Haka nan kuma kungiyar kyautata ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wannan taro a matsayin daya daga cikin kayayyakin tarihi na ruhi na duniya, saboda irin gagarumin taron da ake yi wanda ba wai kawai ‘yan shia ko kuma musulmi ne kawai suke taruwar ba, face har da mabiya sauran addinai ma, wanda ko shakka babu akwai wasu darussa masu yawa cikin hakan.
Daga cikin irin darussan da za a iya gani cikin wannan taro na arba’in shi ne cewa wannan taron wata alama ce da ke bayyanar da wata al’ada ta karfafawa da kuma bayyanar da ‘yan’uwantaka da kaunar juna a tsakanin musulmi da kuma yin watsi da duk wani sabani da ake da shi da haduwa karkashin inuwar Imam Husain da gidan Ma’aiki.
Taron arba’in wata dama ce ta haduwar zuciya waje guda tsakanin musulmi da sake tabbatar wa duniya da kuma masu adawa da Musulunci da gidan Annabta cewa musulmi dai suna bisa tafarkin “mai zaman lafiya da wanda ya zauna lafiya da ku.
Kamar yadda kuma, har ila yau, taron arba’in din wata alama ta haduwar zukata da aiki tare tsakanin al’ummomi daban-daban, kimanin kungiyoyi 7600 suka yi hidima ga masu ziyarar.
Kamar yadda kuma daga kasashen ketar kimanin kungiyoyi ko Haiat 73 suka zo domin yin wannan hidima mai alabarka masu ziyarar arbaeen na wannan shekara, bisa ga bayanin da majalisar gundumar ta fitar, lamari da ke nuni da hadin kan da ke tsakanin musulmi da kuma kaunarsu ga iyalan gidan Annabi.
3459651