IQNA

Ana Ajiyar Kwafin Kur’ani mafi Karanta A Kasar Saudiyyah

23:41 - December 05, 2015
Lambar Labari: 3460124
Bangaren kasa da kasa, ana ajiyar wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da hannu mafi karanta akasar Saudiyya a yankin Ihsa da ke gabacin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «pressarab.net» cewa, tun da jimawa ake ajiyar wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da hannu mafi karanta a yankin Ihsa da ke gabacin kasar kasar saudiyyah.

Wanda ke ajiyawar wannan kwafin kur’ani ya bayyana cewa ya yi kokari matuka domin tabbatar da cewa an ci gaba da adana shi, domin kuwa wannan kwafin kur’ani yana kima da matsayi da bai kamata  ayi wasa da shi ba.

Hussain Alkhalifah shi ne wanda ya mallakin wannan wuri na ajiye kayan tarihi, inda a kuma a nan ne ake ajiye wannan kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da hannu wanda kuma shi ne mafi karanta irinsa.

Ya ce girman kr’anin da fadinsa ya kai cm 4 a cikin ¾, kuma kimarsa za ta kai Riyal dubu 500 na kasar saudiyya.

Daif Al-daif daya daga cikin abokan mutumin da ya mallaki wannan wurin ajiye kayan tarihi ya bayyana cewa, bisa ga binciken da suka gudanar kan wannan kwafin kur’ani, an gane vewa an rubuta shi ne tun  acikin shekara ta 343 hijira kamariyyah.

Ibrahim Zimar shi ma wani mai ajiye kayan tarihi ne, ya bayyan acewa ya ajiye wani kur’ani da aka rubuta da hannu wanda shi ma an rubuta shi a cikin shekara ta 1171 hijira kamariyya, kuma kimar kudinsa ya kai Riyal dubu 250 a halin yanzu.

3459823

Abubuwan Da Ya Shafa: Kuran
captcha