Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na jaridar The Guardian cewa, Doland Trump dan takarar shugabancin kasar Amurka mai jawo hatsaniya ya sake maimaita furucin na kin mabiya addinin muslnci a kasar wanda hakan ke fuskntar kakakusar suka.
Yan siyasa da cibiyoyin kasa da kasa suna ci gaba da tofin Allah tsine ga kalaman nuna adawa ga musulmi da Musulunci da daya daga cikin 'yan takaran shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump yayi na inda ya bukaci a hana Musulmai shiga Amurka gaba daya.
Allah wadai na baya-bayan nan shi ne wanda ya fito daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bakin mai magana da yawun hukumar Melissa Fleming, wacce ta bayyana cewar maganganun da ake yi a yakin neman zaben shugabancin Amurka yana cutar da da shirin majalisar na tsugunar da 'yan gudun hijirar Siriya a Amurkan.
Madam Melissa Fleming ta ci gaba da cewa tun bayan harin da aka kai birnin Paris, da dama daga cikin gwamnonin jihohin Amurkan suka fara magana da kuma bukatar a dakatar da shirin ba wa 'yan gudun hijiran Siriyan matsuguni, wanda a cewarta hakan babban abin kunya ne.
A jiya ne Donald Trump din a yayin yakin neman zabensa ya bukaci da a hana shigowar musulmi zuwa kasar Amurka gaba daya lamarin da ya fuskancin tofin Allah tsine daga gwamnatin Amurka da kuma wasu 'yan takarar shugabancin kasar.
Wadannan kalamai na Trump suna zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurkan tana a kan gaba wajen goyon bayan 'yan ta'addan da suke aikata ta'addanci a kasashen Siriya da Iraki.
3461041