IQNA

An Gno Makeken Kabarin Musulmi A Kenya / Ana Zargin Jami’an Tsaron Kasar

23:43 - December 09, 2015
Lambar Labari: 3461861
Bangaren kasa da kasa, an gano wani makeken kabarin da ake kyautata zaton gawwakin mabiya ddinin muslunci ne a cikinsa a gabacin kasar Kenya kuma ana zargin jami’an tsaron kasr.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa nayanar gizo na Anatoli cewa, lokuta da dama ana zargin jami’an tsaron kasar Kenya da aikata irin wannan ta’asa  akasar a kan musulmi.

Daya daga cikin yan majalisar dattijan kasar da ya fito daga wannan yanki ya bayyana cewa, suna kyautata zaton cewa wannan kabari ya kunshi gawwawakin musulmi ne, domin kuwa akwai dalilai da suke nuni da hakan, kuma ana sa ran jami’an tsaro ne suka kashe suka bizne su a wannan wuri.

Jami’anm tsaron na Kenya dai sukan dauki irin wannan mataki kan mabiya addinin mslunci a wasu yankna na kasar bisa hujjar yaki da ta’addanci, wanda kma hakan bas hi da wata alaka da mutanen da suke rauwa a wadannan wurare.

Wasu daga cikin musulmin yankin sun ce akwai wadanda suka sani wadsanda jami’an tsaro suka kama su kuma bas u kara jin duriyarsu ba, kuma suna sa ran an kashe ne ba tare da wani bincike kan lamarinsu.

Musulmin suna kokawa da cewa ana cin zarafinsu har kashe babu gaira babu sabar, kuma jami’an tsaron gwamnatin kasar ne ke yin hakan ba wasu mutane na daban ba, kma laifinsu kawai shi ne su muuslmi ne, kuma sun sha yin kira amma babu mai taimako.

A cikin shekarar da ta gabata wato 2014 an nuna wa jami’an majalisar dinkin duniya wasu kabruka na musulmi da yan sanda suka kashe a cikin sheakara ta 2010, amma babu abin da ka yi har yanzu kan batun.

Haka nan kuma wasu masu fafutukar kare hakin bil adama sun gano wani kabarin matasa 100 dukkanin musulmi da jami’an tsaro suka kashe, kuma shi ma ba a dau wani mataki kan hakan ba.

3461688

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha