IQNA

Rundunar Sojin Najeriya Ta Tabbatar Da Kama Sheikh Zakzaky

22:26 - December 15, 2015
Lambar Labari: 3463639
Bangaren kasa da kasa, rundunar sojin Nigeriya ta tabbatar da kame Sheikh Yakub Ibrahim El-Zakzaki shugaban Harkar Musulunci a kasar a gidansa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga tashar talabijin ta Press TV cewa, a taron manema labarai da ya gudanar a jiya Litinin a jihar Kadunan Nigeriya; Shugaban rundunar soji ta daya da ke jihar Kaduna Manjo Janar Adeniyi Oyebade ya tabbatar da cewa; Sojojin gwamnatin Nigeriya sun kame Sheikh Yakub Ibrahim El-Zakzaki da matarsa Zeenatu a gidansu da ke unguwar Gyellesu a garin Zariya, inda dukkaninsu biyu suke dauke da raunuka a jikkunansu sakamakon harbinsu da bindiga, amma dai suna raye sabanin rahotonni da suke cewa matarsa ta rasa ranta.



Nusaiba Ibrahim Zakzaki diyarsa ta tabbatar da cewa an kame mahaifin nata kuma yana cikin mawuyacin hali, inda ta bkaci magiyan baynasa da suka shi a cikin adua, kamar yadda kuma ta bayyana cewa wadanda suka aikata hakan suna son tsokana ne domin a yi wani abu sai fake da hakan domin samun hujjar ci gaba da kisan jama’a, a kan tace ya kamata komai ya zama a cikin tsari.



Tun a ranar Asabar da ta gabata ce rundunar sojin Nigeriya ta fara kai farmaki kan magoya bayan malamin  jagoran harkar Musulunci a Nigeriya bisa zargin cewa sun hana tawagar babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar shigewa a garin Zariya, inda ya zuwa yanzu sojojin suka kashe daruruwan magoya bayan Harkar Musulunci ciki har da dan malamin.

Daruruwan 'yan Shi'a a wasu garuruwan arewacin Nigeria suna gudanar da muzahara domin nuna adawa da matakan da sojoji suka dauka a kan 'yan kungiyar a Zariya.

Bayanai sun ce 'yan Shi'a sun bazama a kan wasu tituna a garin Kaduna inda suke korafi kan irin yadda abubuwa suka kasance bayan da sojoji suka kama shugaban 'yan Shi'a, Malam Ibrahim El-Zakzaky tare da wasu mabiyansa.

Rahotanni sun ce an baza jami'an tsaro a wasu manyan tituna da ke Kaduna domin hana afkuwar rikici.





A yanzu haka dai an rufe shaguna da wasu manyan ofisoshi a Kaduna a yayin da aka soma zaman dar-dar, ana cewa mutane kimanin 50 suka rasu, amma dai bisa ga wasu rahotanni adadin ya fi haka nesa ba kusa ba.

Can ma a birnin kano, bayanai sun ce 'yan Shi'a na gudanar da muzahara saboda abin da suka kira muzgunawar da sojojin Nigeria suka yi musu.

Tun bayan da aka soma rikici tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya, bayanai sun ce an hallaka mutane da dama sannan kuma an rusa wuraren ibada na 'yan Shi'a din a Zariya.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Nigeria sun yi zargin cewa an hallaka 'yan Shi'a fiye da daruruwa a lokacin da sojojin suka kai samame a gidan El-Zakzaky a karshen mako a Zariya.



3463552

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha