IQNA

Kungiyar Kare Hakiin Bil Adama Ta Ce Babu Wani Uzuri A Kisan ‘Yan Shi’a Da Sojoji Suka Yi A Najeriya

22:20 - December 23, 2015
Lambar Labari: 3468883
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama da duniya ta bayyana dalilan da sojojin Najeriya suka bayar na kisan ‘yan shi’a a Najeriya da cewa dalilai ne na shirme.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na (hrw.org) cewa, Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya Human Rights Watch, ta ce sojojin Najeriya ba su da wata hujjar kashe 'yan Shi'a a Zaria, duk da ikirarin da suka yi cewa mabiya Shi'ar sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, janar tukur buratai.
A wani rahoto da kungiyar ta fitar ta ce shaidun da ta tattauna da su sun gaya mata cewa sojoji sun kashe 'yan Shia fiye da 300 a kwanakin biyu da suka kwashe suna yi musu luguden wuta.
Human Rights Watch ta ce , "Mun tattauna da shaidu 16 da kuma wasu biyar -- cikinsu har da shugabanni wadanda suka gaya mana cewa sojojin Najeriya sun yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi a cibiyoyi uku na 'yan Shi'a a Zaria daga ranar sha biyu zuwa sha hudu zuwa ga watan ba zai yiwu a ce tare hanyar da 'yan kungiyar suka yi ya zama hujjar kashe daruruwan mutane ba".
Kungiyar ta kara da cewa, "Sojoji sun kai hare-hare kan cibiyar Hussainniya Baqiyyatullah, da gidan shugaban 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Al Zakzaky da gidajen makwabtansa da ke Gyellesu da kuma makabartar 'yan Shi'a a cikin kwanaki biyu. Shaidu sun gaya mana cewa sojojin sun kashe akalla 'yan Shi'a dari uku ko fiye ko fiye da haka".
Haka kuma kungiyar ta ce sojojin sun binne mutanen da suka kashe a manyan kaburbura ba tare da amincewar 'yan uwa da danginsu ba, an kuma ji ra’ayoyin mutane 16 da kuma wasu 5.
Human Rights Watch ta ce dole ne kwamitin da gwamnati ta kafa domin gano musabbabin rikicin ya yi aiki ba tare da nuna son kai ba, tana mai cewa dole ne a hukunta duk mutumin da aka samu da laifi.
Rundunar sojin Najeriya dai ba ta yi raddi kan wannan rahoton ba, sai dai a baya ta sha nanata cewa ta dauki mataki kan 'yan Shi'ar ne saboda sun yi yunkurin hallaka Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai.
Kazalika, rundunar sojin ta sha musanta cewa ta kashe 'yan Shi'a da dama a arangamar da ta yi da su.
Bayanin ya ce abin da sojojin suka yi ya yi hannun riga da doka ta 22 ta majalisar dinkin duniya da ta hana yin amfani da karfi kan fararen hula a kowace kasa ta duniya wadanda bas u dauke da makamai.

 

Duk da cewar dai babu musu ga asarar ran dai rundunar sojan ne dai ke neman hukumar bin bahasin kokari na hallaka shugabanta a hannu na kungiyar.

Abun kuma da a cewar garba mar kari da ke sharhi kan lamuran tsaro da siyasa ya sanya da kamar wuya hukumar tai tasiri wajen tabbatar da gaskiyar da 'yan kasar ke son su ji yanzu.

 

Bincike na hukuma ko kuma kokarin rufe baki, har ya zuwa yanzu dai fadar gwamnatin kasar ta Aso rock na cigaba a karatun na mujiya a cikin kisan da ya dauki fassara daban-daban cikin kasar.

To sai dai kuma a tunanin ministan tsaron kasar Janar mansur sun natsu da nufin zurin ido ga matakin jihar Kaduna da ke da ruwa da tsaki da neman baki na zaren.

 

Abin jira a gani dai na zaman mafitar rikicin da ke zaman sabuwar barazana ga kasar da ke neman fita da kyar cikin rikicin yakin yan ta’adda.

3468841

Abubuwan Da Ya Shafa: HRW
captcha