Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, Shuqi Allam babban mufti na kasar Masar ya bayyana cewa, aya ta 82 daga surat Maidah, tana yin ishara da cewa; wadanda suka fi kusanci da kuma son muminai su ne wadanda suka ce su ne nasara, wati mabiya addinin kirista, saboda a cikinsu akwai malamai masana ruhbaniyawa, wanda hakan a cewarsa na nuna alama ta kauna a tsakanin muslmi da kuma kuristoci.
Ya ce fadin sakon taya murnar kirsimati yana da bababn tasiri wajen karfafa kauna da zaman lafiya atsakanin al’ummomin musulmi da mabiya addinin kirista a ko’ina.
Ya ce babu laifi idan mutum ya taya wani dan kasarsa murna da yake bin tafarkin Catholic, Protestant, Qibdanci ko kuma Angalican murnar haihuwar annabi Isa Almasih (AS) da ma sauran lamurra da suka shafi ranakun da mabiya wannan addini suke girmamawa, domin hakan yana kara karfin zumunci da kauna a Tsakani.
Ya ce saboda isar da sakon taya murnar miladiya ga kiristoci daga bangaren musulmi, ba ma ya halasta ba ne kawai, yana ma da kyau, domin hakan zai kara ganar da kiristociin cewa musulmi ba makiyansu ba ne, yan uwansu ne da suke bin addinin ubangijin Isa da manzon tsira.
3469106