IQNA

Kashe Sheikh Nimr Shiri Ne Na Israel Domin Haifar Da Fitina Tsakanin Shi’a da Sunnah

16:15 - January 09, 2016
Lambar Labari: 3480033
Bangaren kasa da kasa, Ali Faiz wani mai rajin kare hakkin bil adama dan kasar Bahrain mazaunin birnin London ya bayyana cewa kasha Sheikh Nimr tsarin na yahudawa domin haifar da rikcin sunna da shi’a a cikin kasashen musulmi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a zantawa da Ali Faiz wani mai rajin kare hakkin bil adama dan kasar Bahrain mazaunin birnin London ya bayyana cewa kashe Sheikh Nimr ya jefa iyalan gidan Saud cikin matsananci hali na tsaka mai wuya.

Alfaiz ya ci gaba da cewa wannan mummunan akida da take mulkin kasar Saudiyya ta zama guba ga addinin musulunci domin kuwa ta gurbata tunanin musulmi da dama, ta saka kiyayya da gaba a tsakanin musulmi domin biyan bukatun yahudawan sahyuniya.

Babbar manufar yahudawa ita ce kawo Baraka a tsakanin kasashen usulmi da al’ummar musulmi ta hanyar yin amfani da wahabiyanci a cikin duniya, wanda kuma a halin yanzu abin da yake faruwa kenan.

Wanann mai rajin kare hakkin bil adama ya ci gaba da cewa iyalan gidan Al Saud su ne yahudawa suka dora ma nauyin aiwatar da waann shiri na tarwatsa kan al’ummar musulmi bai daya, kuma kisan Sheikh Nimr na daga cikin wannan shirin.

Daga karshe y ace dole ne kasashen musulmi su zama cikin fadaka su gane cewa Saudiyya da yahudawa duk suna aiki guda na raba kan musulmi, abin ban takaici ne kuma yadda ya zama kasar musulmi ce ake amfani da ita domin aiwatar da hakan.

http://iqna.ir/fa/news/3464981


captcha