IQNA

An Bude Taron Bayar Da Matsayin Birnin Al’adun Mulsunci Na 2016 Ga Kuwait

20:24 - January 19, 2016
Lambar Labari: 3480057
Bangaren kasa da kasa, an bude taron mika matsayin babban birnin Ala’adun musulunci ga birnin Kuwait na shekara ta 2016 wanda aka bude a garin Salimiyyah na kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alqabs cewa, a jiya an bude taron mika matsayin babban birnin Al’adun musulunci ga birnin Kuwait na shekara ta 2016 tare da halarta Jabir Mubarar Al Sabah firayi ministan kasar ta Kwait.

Salam Sabah Salim Alhamud Sabah ministan yada labarai na kasar ta Kuwait ya bayyana a wajen bude taron cewa, babban abin alfahari ne ga daukacin al’ummar kasar baki daya yadda suka samu wannan matsayi na ayyana birninsu a wannan matsayi.

Ya ci gaba da cewa wannan ya faru ne sakamakon irin kokarin da Abdulazizi bin Usman Altuwaijari babban sakataren kungiyar yada al’adun muslunci ta duniya ISESCO ya yi ne, da nufin karfafa hadin kan kasashen musulmi.

Ministan yada labaran kasar ta Kuwait ya bayyana wannan a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci da zai taimaka matuka wajen ganin an kara bayyana hakikanin fuskar musulunci mai kyau, sabanin abin da ake yada wa duniya akan muslunci.

Salman Sabah Salim Hammud Sabah ya kara da cewa, za su yi amfani da wannan damar domin kara kusanto da fahimtar juna atsakanin musulmi da sauran al’ummomi da kuma kara yada kauna da sulhu a tsakanin al’ummomi.

Daga karshe ya bayyana cewa abin alfahari ne gare su yadda babban malamin Azahar Ahmad Tayyib ya halarci wannan taro, domin mika matsayin babban birnin al’adun muslunci ga Kuwait na shekara ta 2016.

3468662

captcha