IQNA

Tattauna Matsayin Muslunci Na Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi A Taron Davos Switzerland

20:27 - January 19, 2016
Lambar Labari: 3480058
Bangaren kasa da kasa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa a kasar Masar zai gabatar da jawabi kan matsayin addinin musulunci damgane da tsatsauran ra’ayi da ake dangantawa da shi a taron an Davos.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum sabi cewa, taron na Davos dai za a bude shi gobe Laraba tare da halartar shugabannin wasu kasashe da kuma fitattun mutane daga kasashe kimanin 150 na duniya, inda Shauki Allam zai gabatr da jawabi ga taron.

Shauki Allam zai yi bayani kan matsayin addinin mulsunci wajen kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai, da kuma yadda muslunci yake kin ayyuka na tashin hankali.

Haka nan kuma daga cikin muhimamn lamurran da jawabin nasa zai mayar da hankalia  kansu akwai batun yadda ayyukan ta’addanci suka bata sunan addinin muslunci a duniya, da kuma yadda ya zama wajibi a banbance tsakanin muslunci na gaskiya da kuma ta’addanci.

Shauki Allam kafin barin kasar Masar ya bayyana cewa; wannan taron na Davos babbar dam ace ga musulmi da su bayyana addininsu da kuma koyarwasa ga dunya, maimakon barrin wasu suna Magana da yawun muslunci suna bata masa suna a duniya.

Malamin na Masar zai gana da babban sakararen majalisar dinkin duniya akasar ta Switzerland Banki Moon, kamar yadda kuma zai gana da wasu daga cikin manyan jami’ai da ska shirya taron, gami da jagoran majami’ar Angalican ta kasar Birtaniya.

3468487

captcha