IQNA

Bayanin Cibiyar Yada Al’asun Muslunci Kan Ranar 22 Ga Watan Bahman

23:39 - February 11, 2016
Lambar Labari: 3480127
Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada al’adun mslunci ta fitar da bayani wanda ta yada ta hanyar ofisoshinta a duniya dangane da ranar 22 Bahman.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, cibiyar ta fitar da bayaninta kamar haka:

Da Sunan Allah Ta’ala

Godiya ta tabbata ga Allah da ya shiryar da mu da wannan, ba mu kasance masu shiryuwa da ba don Allah ya shiryar da mu ba.

Shekaru 37 ke nan da samun nasar juyin juya halin musluncia Iran a karkshin jagorancin marigayi Imam Khomeni (QS) wanda ake gudanar a yau a daidai irin wannan rana.

Wannan juyi ya kasance day daga cikin abubwan da ake buga misali da su a cikin wannan karni, domin babu wani makamancin hakan da ya faru a cikin wannan karni na juyi wanda ya zama ya ginu a kan akida ta addini wanda kuma ya bayar da misali a dukaknin bangarori na rayuwa da zamantakewa kamar wannan juyi.

A cikin wadannan shekaru a karkashin jagorancin malamai a bisa mahangar shugabancin malamai da aka fi sani Wilayat Faqih, wanda jagoran juyi na yanzu yake jaddada hakan a matsayin babban rukuni na juyin da sirrin wanzuwarsa, al’umma sun kara zama cikin fadaka a kan addidins da duniyarsu.

Haka nan kuma a karkashin juyin juya halin muslunci a Iran Iran ta samu manyan nasarori a bangarorin ilimin addini da kimiyya da fasaha, kamar yadda kuma ta samu gagarumin ci gaba a fagen fasahar nukiliya da kuma sarra wannan fasaha wajen ayyuka na farar hula, wanda a kan haka aka kakaba takunkumin zalunci, amma daga bisani wadanda suka yi hakan sun gane kurensu.

Daga karshe bayanin na cibiyar yada al’adun muslunci ya jinjinawa jagoran juyin islam da kuma al’ummar kasar ta Iran, tare da kiransu da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin alartar tarukan wannan babbar rana, tare da jaddada matsayinsu na yin riko da addininsu da koyarwarsa da kuma kasarsu da tsarinta na muslunci.

3474716

captcha