
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, al’ummar Bahrain suna gudanar da gangami a dukkanin yankunan kasar domin tunawa da kisan da Al Khalifa suka yi masu shekaru biyar ad suka gabata.
A ranar 14 ga watan Fabrairu 2011 dubban al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da bore na neman yancinsu na siyasa, da kuma hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu na yan kasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da gangamin ana bayar da taken mutuwa a kan Al Khalifa da masu mara musu baya wajen kashe al’ummar Bahrain.
Wadanda suke alaka da suna daukar matakan murkushe masu zanga-zanfga tun bayan da aka fara wannan bore na lumana domin neman hakkokinsu, tare da kame su da saka su a cikin gidan kurkuku suna azabtar da su azaba.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasar sun cewa, a cikin wannan shekaru biyar masarautar Al Khalifa ta kasha mutane fiye da 160, da suka hada da mata da kanan yara da tsoffi, saboda dalilai na siyasa da murkushe muryar al’ummar kasa mai neman yancinta na siyasa.