IQNA

16:53 - February 16, 2016
Lambar Labari: 3480144
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani jerin gwano domin nemana saki Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran yan shi’a a Najeriya da ake ci gaba da tsare shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Post cewa, an gudanar da wanann zanga-zanga ne a garin Bauchi, wanda kuma mafi yawan wadanda ke cikinta mata ne.

Haka nan kuma an gudanar da wata irinta a ranar lahadi da ta gabata, a biranan Kaduna da Yawuri, inda ake yin kira ga mahukuntan tarayyar najeriya da su gaggauta sakin Shehin malamin da suke tsare da shi.

Tun a cikin watan disamban karshen shekarar da ta gabata ne dai jami’an sojin najeriya suka kai farmaki kan gidan Sheikh Zakzaky da wuraren da yan shi’a suke gudanar da taruka, inda suka kasha daruruwa daga cikin tare da kame malamin nasu.

Baya ga najeriya ana ci gaba da gudanar da irin wanan zanga-zanga ta yi Allawadai da wannan danyen aiki na kisan kiyashi da sojojin najeriya suka yi kan fararen hula marassa makami.

3476060

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: