IQNA

Mahardata 12 Sun kai Ga Matakin Kusa Da Na Karshe Gasar Kur’ani Ta Aljeriya

23:34 - February 23, 2016
Lambar Labari: 3480168
Bangaren kasa da kasa, kimanin mahardata 12 ne suka kai ga matakin kusa da na karshe a gasar kur’ani ta Aljeriya da ake watsawa atashar Al-shuruq TV.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na echoroukonline.com cewa, tun a ranar Juma’a da ta gabata ce aka fara gudanar da wannan gasa ta kur’ani mai tsarki da tashar Al-shuruq TV take watsawa kai tsaye tare da mahardata 23m yanzu kuma 12 ne suka kai ga matakin kusa da na karshe.

Wadanda suka samu nasarar kaiwa ga wannan mataki sun fito ne daga yankunan Aljazeera, Sutaif, Mustagnam, Warqala, Buwara, Madira, Sidi Bil Abbas, Tilmisan, Na’ama, Batana, Sikada.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta kayartar matuka ga al’ummar kasar da suke binta kai tsaye ta hanyar tashar talabijin da ake watsawa.

Tashar talabijin ta Al-shuruq TV ita ce dai take daukar nauyin watsa wanann gasa, wadda kuma ta kunshi matasa ne yan kasa da shekaru 15 daga sassa na kasar.

Ridwan Hussain daya ne daga cikin wadanda sukekula da shirya wannan gasa, ya bayyana cewa akwai daruruwan wadanda suka bayyana bukatarsu ta neman a dauke su domin shiga wannan gasa, to amma adadin da ake bukata kayyadade ne, saboda haka daga karshe mutum 50 ne kawai suka dauka.

An dai kasa bangarorin gasar da kuma yadda ake gudanar da ita, inda a bangaren farko akan fara da masu hardar dukkanin kur’ani mai tsarki, daga bisani kuma biyo kasa da hakan.

A cikin watan Ramadan mai alfarma wannan tasha tana shirya wata gasa ta kur’ani mai tsarki, inda ake samun halartar daruruwan makaranta, daga bisani kuma ta bayar da kyautuka.

Dagha cikin kyautukan dai har da bayar da kujerar zuwa Makka da Madina ziyara ga matsayi na farko, sai kuma a matsayi na biyu zuwa Turkiya, na uku kuma zai tafi kasar Tunisia.

3477572

captcha