IQNA

Koyar Da Karatun Kur’ani mai Tsarki Ga “yan mata A London

23:48 - March 29, 2016
Lambar Labari: 3480272
Bangaren kasa da kasa, cibiyar gudanar da ayyukan alkhari ta Nur ta dauki nauyin gabatar da shirin horar da yan mata karatun kur’ani a London.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, wannan shiri za a rika gudanar da shi ne a dukaknin ranakun laraba.

Daga cikin abubuwan da shirin zai kunsa har da koyar da karatun kur’ani da kuma koyar da hukuncin karatun ga ‘yan matan da suke halarta.

Shirin zai kunshi yan mata ne masu shekaru daga 10 zuwa 16, wadanda malama Wujdan haidar malamar kur’ani za ta rika gabatar musu da tilawa suna koyo, tare da tabbatar da cewa suna bin salon sahihin karatun.

Babbar manufar wannan cibiya da ta kirkiro da shiri wato cibiyar Nur shi ne, koyar da karatiun kur’ani gay an mata musulmi, musamman ma ganin cewa suna zaunea kasar da hakan zai yi musu wuya, inda kuma samar da wannan hanya zai taimaka ma iyayensu wajen ganin sun tarbiyar da yaransu kan koyarwar kur’ani mai tsarki.

3484770

captcha