IQNA

Wakiliyan Majalisar Dinkin Duniya Me Tace A Hubbaren Imam Hussain (AS)

23:26 - April 03, 2016
Lambar Labari: 3480288
Bangaren kasa da kasa, Liz Grand babbar wakiliyar majalisar dinkin duniya a kasar Iraki ta bayyana cewa ta samu wata irin natsuwa alokacin da ta shiga hubbaren Imam Hussain (AS)

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren kula da hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, a lokacin da Liz Grand babbar wakiliyar majalisar dinkin duniya a kasar Iraki ta shiga hubbaren Imam Hussain (AS) ta bayyana cewa ta samu wata irin natsuwa ba ta misiltuwa.

Ta bayyana cewa hakika wannan wuri yana da wani matsayi na musamman a wurinta, domin kuwa ya yi tasiri matuka a cikin rayuwarta, domin ta samu wata natsuwa da karfin ruhi na musamman a lokacin da ta saka kafarta awurin.

Haka nan kuma ta kara da cewa, babbar manufar kai ziyara a wannan wuri mai tsarki ita ce gudanar da ayyuka na jin kai na taikama ma mutanen ad suka yi gudun hijira daga yankunasu domin tsira daga harin yan ta’adda.

Ta ce ko shakka babu za su yi aiki tare da bangaren kula da wannan hubbare mai tsarki wajen taimakon yan gudun hijira, domin kwa sun samu dukkanin irin goyon bayan da suke bukata domin gudanar da wannan babban aiki daga wannan bangaren na kula da hubbaren mai tsarki.

3485470

captcha