Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, sakamakon
abin da kafifin yada labaran kasar ta Sweden suke bugawa kyamar musulmi ta karu
matukaa kasar, wanda hakan ya sa suka yi gangami a fadar mulkin kasar.
Masu gangamin sun yi ta rera taken neamna dauki matakan da suka dace domin kare hakkokin musulmi akasar, wadanda suke fuskantar cin zarafi saboda addininsu.
Daya daga cikin masu gudanar da wannan zanga-zanga ya sheda cewa, sun taru ne domin nuna takaicin kan yadda ake takura msuulmi da tozartasu a kasar da ke da'awar yancin bil adama da dimokradiya a nahiyar turai.
Abin tuni a nan dais hi ne a cikin kwanakin nan wasu daga cikin kafofin yada labarai na kasar Sweden musamamn ma mujallau da kuma jaridu, sun sako msulunci a gaba, inda suke bayyana shi da cewa a ddinin ne na ta'addanci.