Kamfanin dillancin labaran kur’ani
na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin yau
Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei
ya gana da shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye da ‘yan tawagarta da
suka kai masa ziyarar ban girma a ci gaba da ziyarar da take yi a Iran, inda
yayin da yake ishara da mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta karfafa
alaka da kasashen Asiya, Jagoran ya bayyana cewa ‘ci gaba da karfafuwar alaka
tsakanin Iran da Koriya wani lamari ne da zai amfani dukkanin kasashen biyu.
Daga nan sai Jagoran ya ce: Wajibi ne yarjejeniyoyin da za a kulla tsakanin
kasashen biyu su zamanto ta yadda haraji da takunkumin da aka sanya ba za su
yi mummunan tasiri kan su ba. Don kuwa bai kamata a ce manufar Amurka ta yi
tasiri cikin alakar da ke tsakanin kasashe irin su Iran da Koriya ta Kudu ba.|
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar musayen kwarewa a bangarori daban-daban da suka hada da ilimi, fasaha, siyasa, zamantakewa da kuma tsaro tsakanin kasashen Iran da Koriya ta Kudu wani lamari ne da zai amfani dukkanin kasashen biyu, don haka sai ya ce: Mu dai a siyasarmu ta waje mun fi karkata zuwa ga kasashen Asiya saboda tarayyar da muke da ita a fagen al'adu da tarihi. A saboda haka ne muka yi amanna da cewa yiyuwar cimma fahimtar juna da aiki tare da wadannan kasashen ciki kuwa har da kasar Koriya ta Kudu, wacce tana daga cikin kasashen da suka ci gaba a Asiya, ta yi girma da yawa. Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin matsaloli na tsaro da ake fuskanta a yankin nan da ma duniya baki daya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Matukar dai ba a yi fada da rashin tsaro da kuma ta'addancin da ake fuskanta ta hanyar da ta dace ba, to kuwa a nan gaba maganin hakan zai yi wahalar gaske, sannan kuma babu wata kasar da za ta tsira daga wannan hatsarin. Har ila yau kuma yayin da yake magana dangane da raba ayyukan ta'addanci zuwa gida biyu, mai kyau da mara kyau, da Amurka ta yi, Jagoran ya bayyana cewar: Amurka dai tana rera taken fada da ta'addanci, to amma a aiki kan ba da gaske take yi ba. Don kuwa ta'addanci a kowane yanayi nasa, lamari ne mai muni sannan kuma hatsari ne ga al'ummomi da kuma tsaron kasashe. Don kuwa matukar aka rasa tsaro, to kuwa ba za a samu irin ci gaban da ake bukata ba. Yayin da yake magana dangane da yarjejeniyoyin aiki tare da aka cimma tsakanin kasashen biyu kuwa, Ayatullah Khamenei yayi ishara da batun abubuwan da ya kamata kasashen biyu su fi ba su muhimmanci inda ya ce: Akwai damar kulla yarjejeniya aiki tare da za ta amfani kasashen Iran da Koriya ta Kudu, to amma abin da muka fi ba shi muhimmanci a fagen aikin tare ba wai kawai shi ne fagen kasuwanci ba, face dai wajibi ne yarjejeniyoyin da za a sanya wa hannu su zamanto abubuwan da Iran take bukatarsu ne wajen gina kasa da tattalin arziki na al'umma. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana rashin tasirin abubuwan da za su kunno kai daga waje cikin yarjejeniyoyin da aka cimma a matsayin daya daga cikin abubuwan da ya wajaba a yi la'akari da su cikin alaka da aiki tare tsakanin kasashen biyu yana mai cewa: Bai kamata alakar Iran da Koriya ta Kudu ta zamanto ta damfaru da takunkumi da kuma tasiri da manufar Amurka ba, face dai wajibi ne alakar kasashen biyu ta zamanto mai dorewa kana kuma karfafaffiya. Haka nan kuma yayin da yake ishara da dadaddiyar alaka, amma wacce take cike da kwan gaba kwan baya, da ke tsakanin kasashen biyu, Jagoran ya bayyana cewar: Abin farin cikin shi ne cewa a halin yanzu gwamnatin Koriya ta Kudu wata gwamnati ce da take ba da hadin kai, sannan kuma Iran, kasa ce wacce take da kafafe da dama masu yawa irin su kwararrun matasa masana wadanda suke da karfin taimakawa wajen tabbatar da irin wannan kyakkyawar alaka. Ita ma a nata bangaren, shugabar kasar Koriya ta Kudun Park Geun-Hye wacce shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yake wa jagoranci ta bayyana ziyarar da ta kawo Iran a matsayin wata babbar ta fadada alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma kara yarda da juna, tana mai cewa: A zamanin da Iran take karkashin takunkumi, mun yi iyakacin kokarinmu wajen ganin mun ci gaba da kasantuwa a Iran. Shugabar kasar Koriya ta Kudun ta bayyana Iran a matsayin kasa da take da karfi na al'umma da kuma fagagen da za a iya aiki tare inda ta ce: Muna fatan a nan gaba alakar da ke tsakanin kasashen biyu musamman a fagen tattalin arziki za ta ci gaba da fadaduwa. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da mahangar Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da batun fadaduwar tattalin arzikin Iran haka nan kuma da jaddadawarsa kan fadaduwar ilimi, tattalin arziki da masana'antu bisa tushen dogaro da kai, Madam Park Geun-Hye ta bayyana cewar: Ina da yakinin cewa jaddadawarka kan batun ci gaban tattalin arzikin Iran, lamari ne da zai amfani kasarku, sannan mu kuma a shirye muke mu ci gaba da karfafa alakarmu a bangarori daban-daban da suka hada da yanayi, ilimi da fasaha da kuma tattalin arziki. |