Kamfanin dillancin labaran Iqn aya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaqna cewa,
babbar kotun kolin kasar Bangaladesh ta tabbatar da hukuncin kisa kan Muti
Rahman Nizami jagoran kungiyar Jama’at
Islami babbar kungiyar musulmin kasar.
Bayanin y ace kotun ta dauki wannan mattakin ne bayan da taki amincewa da a dauakak kara bayan da ta sanar da yanke hukuncin kisa a kans Muti Rahman Nizami.
An yanke wannan hukuncin ne bias zarginsa da hannu a ayyukan kasha-kashe a kasar tun bayan da kasar ta samu yancin kanta a cikin shekara ta 1971, inda ya jagoranci wata kungiya da ta yi ta kashe masana da fitattu mutane na kasar, kumakungiyar tana da alaka da Pakistan.
Da dama daga cikin masu karre hakkin bil adama a kasar dai suna ganin cewa wannan hukuncin an siyasa ne kawai.
Muti Rahman Nizami dan shekaru 73 da haihuwa, ya kasance shugaban kungiyar Jama’at Islami tun daga 2000,kuma a tsakanin 2001 zuwa 2006 ya zama minister a lokacin da aka kafa gwamnatn hadin kan kasa.