
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, a yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, Tashar telbijin din Almanar ta nakalto Shugaban kungiyar Gwagwarmaya ta Hizbulah Sayid Hasan Nasrullah na bayyana irin ta'addancin da haramcecciyar kasar Isra'ila ta yi a yankin inda ya ce a kullun magabatan HKI na iya kokari tare kuma da ci gaba da sanya rikici a yankin, amma abin mamaki wasu kasashe suna son gabatar da su a matsayin aminnansu.
A yayin da yake jawabi a kusa da kabarin Shahid Sayid Abas Musawi tsohon shugaban kungiyar Hizbulah a yankin Baka'a dake gabashin kasar ya ce nasorin da kunigiyar gwagwarmayar ta samu a kan Haramcecciyar kasar Isra'ila musaman ma ta shekarar 2000 sun zamanto wani bangare na tarihin da kuma ci gaban kasar Labnon.
Hasan Nasrullah ya kara da cewa Nasarar gwagwarmaya a yau ita ce arzikin kasar Labnon, ga wadanda suka rufe idanunsu ga wannan babban nasara ya kamata su ajiye babbanci da kuma rikicin siyasa a gefe.
Yayin dake bayyani kan halin da kasar ke ciki Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa a halin da ake cikin kungiyar gwagwarmaya na aiki kafada da kafada tare da dakarun kasar domin kare kasar Labnon
Yayin da ya koma kan matakan da wasu kasashen Larabawa suka dauka na kusanci da HKI domin kifar da Kungiyar Hizbulah, Sayid Hasan Nasrullah ya ce duk wanda bai yi imani da gwagwarmaya ba to abinda muke bukata daga kare su su daina yiwa kungiyar zagon kasa.
Yayin da ya koma kan yakin da ake yi a yankin, Sayid Hasan Nasrullah ya tabbatar da cewa ko shakka babu gwagwarmaya za ta ci nasara a wannan yaki kuma zai kasar yankin Palastinu shi kadai fagen gwagwarmaya nan gaba a yankin.
A ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2000 ne kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulah ta tilastawa HKI bada kai gami da ficewa daga kudancin kasar Labnon duk da irin karfin sojan da take da shi.