Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum abi cewa, wananns hiri zai gudana
ta hanyar yin bayani dalla-dalla da harsunan kasashen ketare ga masu fahimtar
wadannan harsuna dangane da abin da ake kira jihadi a addinin muslunci.
Bayanin ya ce shirin zai mayar da hankali ta hanyoyi na yanar gizo domin bayar da bayanai da suka dace a kana bin da ake yada a kan jihadi a mahangar addinin muslunci, wanda kuma hakan yana jawo mummuanr fahimta dangane da wannan addini da kuma bata masa suna aduniya.
Akwai matas kimanin 50 wadanda aka ba su horo a cibiyar muslunci ta Azahar dangane da yadda ya kamata su yada abin da ake bukata a cikin wadandannan harsuna wadanda suke da kwarewa a cikinsu, da nufin wayar da kai.
Wasu daga cikin masu gurbatacciyar akida daga cikin msulmi suna yaudarar matasa musamman daga cikin musulmi da sunan addini ko dogaro da ayoyin kur'ani wajen aikata ta'addanci a duniya, wanda hakan ya sabawa koyarwar muslunci baki daya.
Gyara tunain matasa dangane da mahangar muslunci a kan addini musaman jihadi shi ne babbar manufar wannan shiri, wanda za afara shi a cikin kwanaki masu zuwa.