IQNA

Musulmin Uganda Sun Bukaci A Kirkiro Ma'aikatar Kula Da Harkokin Muslunci A Kasar

23:45 - July 28, 2016
Lambar Labari: 3480653
Bangaren kasa da kasa, Musulmin kasar Uganda sun bukaci shugaban kasar Yoweri Museveni da ya kirkiro da a'aikatar da kula da harkokin muslmi da muslunci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na All Africa ya bayar da rahoton cewa, shugabannin musulmin kasar ta Uganda ne suka gabatar da wannan bukata ga mahukuntan kasar, ganin cewa adadin musulmi a kasar ya kai miliyan 10 a halin yanzu, wato kusa kashi daya bisa uku na al'ummar kasar baki daya, duk kuwa da cewa dai shugaba Yoweri Museveni bai ce komai a kan batun ba.

A kwanakin baya shugaba Yoweri Museveni ya gabatar da wani jawabi a cibiyar zakka ta musulmi da ke birnin Kampala fadar mulkin kasar, inda ya jinjina wa musulmi dangane da tsarin da suke da shi na tattara zakka, tare da yin amfani da ita wajen taimaka ma marassa galihu, inda ya ce hakan lamari ne mai matukar muhimamnci ga tattalin arzikin kasar Uganda.

Idris Lusawabi shi ne shugaban cibiyar musulmi ta kasar Uganda, ya bayyana cewa sun yi farin ciki da yadda shugaban kasar ya a yaba da tsarinsu na zakka da kuma yadda yake bayar da muhimmanci ga lamarin da ya shafi musulmi, kuma suna jiran su jawabinsa dangane da bukatarsu ta kirkiro ma'aikata ta musamman wadda za ta rika kula da harkokin musulmin kasar.

3518435

captcha