Tun a cikin shekara ta 2005 ce jagororin musulmi a kasar ta Singapore suka gabatar da wani tsari na tantance malamai da suke koyar da yara da kuma matasa a cikin makarantunsu, amma sakamakon yadda a kan tura wasu su yi karatu a wasu kasashen larabawa, sukan dawo dauke da wasu akidu na kafirta sauran musulmi da kiransu mushrikai da sauransu, kuma suna yada hakan a tsakanin musulmi, da kuma saka irin wadannan akidua cikin manhajar koyarwa amakarantu.
A baya-bayan nan dai an kame wasu daga cikin matasan musulmin kasar ta Singapore da suke da alaka da kungiyar 'yan ta'addan ISIS, wasu sun hade da mayakan kungiyar a kasashen da take yaki, yayin da kuma wasu aka kame su suna shirin tafiya, bayanin ya ce dukkanin wadanda aka kame suna shirin tafiya jihadi suna daga cikin wadanda suka yi karatun addini ne a wasu kasashen larabawa.
Bayanin malaman ya ce ya zama wajibi a sanya ido domin tabbatar da cewa abin da ake koyar da yara bai yi hannun riga da koyarwar muslunci ba, tare da hana yada akidar kafirta musulmi.