Ya ce kafa wannan doka zai takura malaman addini da sauran masana, alhali kasar Sudan kasa ce ta musulmi wadanda suke bukatar fadakarwa akowane lokaci, kuma mutane suna da masaniya kan addini, a duk lokacin da wani ya kauce a maganar addini a na take za su gane.
A kan haka malamin y ace majalisar tasu tana mika kira ga mahukuntan kasar da su janye wannan doka, amma kuma za a iya saka wasu hanyoyi na tantance abin abi da mutane uke fada, domin tabbatar da cewa ba a yada wai abu da ya kauce ma koyarwar muslucni ba, amma ba hana Magana kan addini ba baki daya sai da izinin gwamnati.
Babbar manufar gwamnatin Suda ta kafa wannan doka dai ita ce hana yaduwar kidar ta'addaci, wadda masu dauke da akidar kan yi amfani da hanoyin wa'zi wajen cusa wannan mummunar akida ta kafirta musulmia cikin zukatan matasa musamman, wanda hakan daga bisani ya kan kai matasa zuwa ga shiga ta'addanci da sunan addini.
3524813