IQNA

Ahmad Umar Hashim:

Gasar Kur’ani Ita Ce Amsa Ga Masu Keta Alfarmar Kur’ani

19:40 - September 22, 2016
Lambar Labari: 3480801
Bangaren kasa a kasa, tsohon shugaba cibiya Azahar ya bayyana gudana da gasar kur’ani ma sarki a matsayin hanyar mayar da martan ga mas keta alfamar wannan littafi mai tsariki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga jaridar Alwatan ta Masa cewa, Ahmad Umar Hashim a yayin girmama wasu daliban kur’ani ya bayyana cewa, hakika gudanar da gasar kur’ani ma sarki a matsayin hanyar mayar da martan ga masu keta alfamar wannan littafi mai tsariki a koina cikin fadin duniya.

Malamin ya nuna farin cikinsa matuka danane da ci gaban da ake samua acikin kasashen musumi ta fuskar raya lamarin kur’ani, da hakan ya hada da gudana da gasa a bangarori daban-daban da suka hada da harda karatu da kuma sanin hukuncinsa.

Ya ce ya saurari karatun dukkanin daliban da suka shiga cikin gasar , kuma babu kure a cikin karatunsu da hardarsu, wanda hakan babban abin alfahari ga al’ummar Masar da ma musulmi baki daya.

Haka nan kuma ya yi kira ga bangarorin da ke daukar nauyin shirya gasar kur’ani a kasar da su zama cikin fadaka a kowane lokaci, kan cewa abin da suke yi aiki ne mai matukar muhimmanci, domin kuwa a halin yanzu wannan ita ce hanya ta mayar da martini ga masu gaba da kur’ani.

Kimanin daibai 27 ne dukkaninsu yan mata suka samu nasara a gasar, inda suka samu kyautuka daga jami’an da suka dauki nauyin shirya gasar da kuma wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halrci wurin.

Hilal Sharbini ministan ilimi na kasar da Muhammad Mukhtar Juma’a ministan kula da harkokin addini, Usam Alabd shugaban kwamitin kula da harkokin majalisa, Usama Alazhari babban mai bayar da shawara kan harkokin addini ga shugaban kasa duk suna cikin wadanda suka halarci wurin.

3531943


captcha