IQNA

Trump Ya Kara Jawo Ma Musulmi Bakin Jini A New Jersey

23:19 - September 27, 2016
Lambar Labari: 3480812
Bangaren kasa da kasa, sakamakon maganganu da Donal Trump dan takarar shugabancin Amurka ke yi ya kara jawo ma msuulmi bakin jinni a jahar New Jersey ta kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Fax News cewa, masallacin Pasic da ke cikin jahar New Jersey ya fuskanci farmaki sakamakon kalaman Donal Trump dan takarar shugabancin kasar Amurka a zabe mai zuwa.

Omar Awad shi ne mai kula da harkokin masallacin wannan gari ya bayyana cewa, tun bayan da aka kai harin satumba musulmi kimanin dubu 2 da suke rayuwa a wannan gari suka fara fuskantar matsaloli.

Sai dai kuma a cewarsa bayan da dan takarar shugabancin kasar Amurka na jamiyyar republican ya fara yin kalaman batunci kan muuslmi abin ya kara muni fiye da kowane lokaci a baya.

Ya ci gaba da cewa, a baya suna zaune tare da mutane da dama da suka fhimci cewa ba dukkanin musulmi ne suka yarda da abin da yan ta’adda suke aikatawa ba, amma kuma bayan taron da ya jagoranta na tunawa da harin 11 ga satumba a yankin, kymar musulmi ta karu matuka fiye da kowane lokaci.

Haka nan kuma ya yi kira ga mahukunta na kasar Amurka da su yi wa musulmi adalci, domin kuwa abin da yake faruwa bas hi da wata alaka da addinin muslunci, kuma yan ta’adda kowa ya sanya, ya san kasar da ke daukar nauyinsu da yada akidarsu, kuma wannan kasar ita ce ma babbar kawar Amurka a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Sau 4 ne aka kai hari kan musulmi a cikin shkara ta 2014, amma a hain yanzu a kowane okaci musulmi ya fita yana cikin halin zullumi, domin za a iya kai masa hari, musamman ma mata da suke dora dan kwali a kansu, wadanda su ne suka fi fuskantar irin wannan matsala.

3533226


captcha