Bangaren kasa da kasa, jami’ar Almustafa (SAW) reshen Senegal ta gudanar da wani shiri na bayar horo kan iyalan gidan manzo ga kananan yara a kasar.
Kamfanin
dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na na jami’ar cewa, an gudanar da wannan horo ne da nufin sanar da yara
hakikanin koyarwar iylan gidan manzon Allah (SAW) a kasar, wanda kuma hakan ya
samu karbuwa matuka.