IQNA

Rashin Bayar Da Halasci Ga Azzalumai Na Daga Cikin Darussan Ashura

23:37 - October 04, 2016
Lambar Labari: 3480822
Bangaren kasa da kasa, Majid Milad daya daga cikin masu gwagwarmaya da kama karya a Bahrain ya bayyana Ashura a matsyin daya daga cikin darussan kin bayar da halasci ga dagutai.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bahrain alyaum cewa, Majid Milad daga cikin jagororin jam’iyyar Alwifaq da masarautar kama karya ta Bahrain ta rusa, ya bayyana cewa Ashura tana koyar da darasi babba dangane da kin mika wuya ga azzalumai.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu masu mulkin kama karya a kasar Bahrain sun fahimci abin da ashura take koyar da mabiya tafarkin iyalan gidan manzo, na kin mika wuya ga duk wani nauin zalunci da danniya irin ta azzaluman mahukunta, a kan haka suka dauki mataki hana gudanar da duk wani abu da ya shafi ashura a kasar, wadda akasarin mutanenta mabiya tafarkin Imam Hussain (AS) ne.

Dangane da rawar da malamai ya kamata su taka kuwa, ya bayyana cewa hakika malamai masu bin tafarkin koyarwar manzo da iyalan gidansa, su ne a sahun gaba wajen fadakar da al’ummar musulmi babban abin da ashura take koyar da su, kamar yadda uma darasinta ya hada yan adam baki daya, da suke son su rayu cikin yanci.

Abin tuni a nan dais hi ne Majid Milady a kasance daya daga cikin manyan jagorori na jam’iyyar siyasa mafi girma atarihin kasar Bahrain ta Alwifaq, wanda ya mika godiyarsa ga Allah madaukakin sarki, kan yadda ya zama daya daga cikin masu fada da zalunci a cikin kasarsa, wanda a kan haka an daure shi tsawon shekara guda a gidan kaso.

3535411


captcha