IQNA

Ammar Hakim Ya Mayar Da Martani Kan Kisan kiyashin Saudiyya A Yemen

20:54 - October 10, 2016
Lambar Labari: 3480844
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Ammar Hakim ya mayar da martini mai zafi kan kisan kiyashin da Saudiyya take yi kan fararen hula musulmi a Yemen.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alfurat cewa, Sayyid ammar hakim shugaban majalisar koli ta musluncia Iraki ya yi Allawadai da kakkausar murka kan kisan gillar da masarautar 'ya'yan saud ta yi kan musulmin kasar Yemen a wannan mako.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kungiyar huthi cewa ya yi, wannan kisan kiyashi ya kara fito da hakikanin fuskar wannan masarauta ta 'ya'yan Saud da turawa suka kafa a cikin kasar hijaz wadda ba ta da aiki sai haifar da fitina da da yaki da kashe-kashe a tsakanin musulmi, tare da rarraba kawunansu, wanda a lokuta da dama tana yin amfani da kungiyoyin ta’addanci da ta kafa ne masu dauke da akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi, inda suke kashe dubban musulmi ba ji ba gani da sunan jihadi, kamar yadda kowa yake gani a wasu kasashen larabawa da na musulmi.

Amma a kasar Yemen masarautar Saudiyyah da kanta ne take aiwatar da wannan ta’addanci kan mata da kananan yara da tsoffi, tare da rusa makarantu da masallatai, asibotoci, kasuwanni da gidajen jama’a, kuma duk hakan yana faruwa ne a kan idanun manyan kasashen duniya, wanda ma wasu daga cikinsu kamar Amurka da Birtaniya ba su boye ma duniya ba kan cewa suna taimaka ma Saudiyya wajen kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen.

Ya kara da cewa wannan babban abin kunya ne wanda ya kara zubatar da martabar manyan kasashen duniya da kuma majalisar dinkin duniya, domin a cewarsa hakan ya tabbatar wa dukkanin al’ummomin duniya cewa maslahar manyan kasashe ita ce a gabansu, ba rayukan jama’a ko hakkokinsu ba, domin kuwa matukar za su kwashi mai a Saudiyya, kuma masarautar kasar za ta ci gaba da yi musu cinikin makamai, babu abin da ya dame su da adadin rayukan da za ta kashe, a Yemen ne ko a ko a wata kasa daga kasashen musulmi da na larabawa.

3537046


captcha