IQNA

Ahlu Sunna A Iraki Suna Gudanar Da Makokin Ashura

23:19 - October 11, 2016
Lambar Labari: 3480846
Bangaren kasa da kasa, Kimanin tawagogi 40 ne na ahlu sunna suke gudanar da tarukan makokin shahadar Imam Hussain (AS) a Dayali Iraki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, Ahmad Tahir shugaban kwamitin kula da tarukan ashura a lardin Diyala ya bayyana cewa, akwai tawagogi 670 ‘yan sunna suna sahun gaba wajen shirya tarukan ashura a lardin inda tawaga 40 daga cikin nasu ne.

Ya ce ko shakka babu a wannan karon an samu gagarumin canji a tarukan da ake gudanarwa a Iraki na ashura, inda lamarin bai takaitu da yan shi’a ba, yan sunna da dama sun shiga cikin lamarin ana yi tare da su.

Ahmad tahir ya ce yan sunna a Iraki sun yi imanin cewa, lamarin Imam Hussain (AS) lamari ne na dkkanin musulmi bay an shi’a kadai ba, saboda haka ba a bar su a bay aba wajen raya wannan taro mai albarka na tunawa da shahadar jikan manzon Allah da iyalan gidan manzo.

3537323


captcha