Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane sha hudu ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai masu taron juyayin Ashura a arewacin kasar.
Hukumomi a lardin Balkh dake arewacin kasar ta Afganistan sun ce mutane akalla sha hudu ne suka rasa rayukansu kana wasu ashin da takwas suka raunana a yayin harin da aka kai a harabar masallacin inda aketaron juyayin Ashura, kamar yaddakakakin gwamnan yankin,Munir Ahmad Farhad, ya shaidawa masu aiko da rahotanni.
Kafin hakan dai mutane sha bakwai ne suka rasa rayukansu kana wasu sittin da biyu suka raunana a wasu masallatai 'yan shi'a biyu da yammacin jiya Talata.
Tuni dai kungiyar 'yan ta'addan daesh ta dauki alhakin kai daya daga cikin harin.
Yau ne dai duniyar musulmin shi'a ke juyayin ranar goma ga watan Muharam wace akafi sani da Ashura wace tayi daidaida ranar da Ummayawa karkashin jagorancin Yazidu sukayi wajikan Manzon tsira Muhammad wato Imam Hussain da iyalansa kisan gilla a garin Karbala na kasar Iraki.