IQNA

UNESCO: Masallacin Aqsa Mallakin Musulmi Ne

21:26 - October 14, 2016
Lambar Labari: 3480856
Bangaren kasa da kasa, hukumar UNESCO ta gabatar da wani daftarin kudiri a gaban kwamitin majalisar dinkin duniya kan mallakar masallacin Aqsa.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin alahad cewa, UNESCO ta bayyana cewa masallacin bas hi da alaka da yahudawa, mallakin musulmi ne.

Hukumar ta mika daftarin kudiri ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wand aka kada kuri’a a kansa, tare da halartar wakilai na kasashen mambobin kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar.

Kasashe 24 sun amince da daftarin kudirin, yayin da kasashe 6 suka ki amincewa da shi baki daya, da suka hada da Amurka da kuma Birtaniya, sai kuma kasashe 26 da suka kada kuri’a baki daya.

Daftarin kudirin ya yi kakakusar suka dangane da yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take iko da wurare masu tsarki mallakin musulmi da kiristoci da suke cikin Palastinu.

Wannan daftarin kudiri ya harzuka manyan jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman ma firayi ministan haramtacciyar gwamnatin yahudawan Benjamin Netanyahu, wanda ya sanar da yanke alaka da hukumar.

Kasashen Algeriya, Morocco, Lebanon, Masar Oman, Qatar, da kuma Sudan su ne suka shirya wannan daftarin kudiri tare da mika shi ga hukumar ta UNESCO.

Yanzu haka dai hukumar ta UNESCO na shirin kara gabatar da wannan daftarin kudiri domin a akara kada kuri’a a mataki na karshe a kansa.

3537564

captcha