IQNA

Shirin Raba Kwafin Kur’ani Dubu 80 A Tanzania

23:12 - October 31, 2016
Lambar Labari: 3480895
Bangaren kasa da kasa, cibiyar bayar da agaji ta RAF a kasar Qtar ta dauki nauyin raba kwafin kur’anai guda miliyan 1 a fadin duniya, inda dubu 80 daga ciki za a raba su a Tanzania.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alarab cewa, wadannan kwafi dbu 80 ana raba su ne ga cibiyoyin addini da kuma makarantun kur’ani da ke kasar.

Abdulnasir Al Fakhur mataimakin shugaban shirin ya bayyana cewa, bisa la’akari da bukatar da ake da ita wannan kasa ta Tanzania zuwa ga kwafin kur’anai, an ware wannana adadi gare su, kuma yanzu haka a cewarsa an fara shirin tarjama wani adadi mai yawa na kur’ani, inda yanzu haka an tarja kwafi dubu 120 a cikin harsuna daban-daban.

Ya kara da cewa babbar manufar shirin shi ne yada kur’anaia akasashen duniya kimanin guda 50, da suka hada da kasashen Afirka, turai da kuma Asia.

Bisa ga wannan shiri kwafi dubu 505 zaa raba su a kasashen Afirka, dubu 40 a Mauritania, dubu 40 a Kenya, dubu 40 a Ugandam dubu 40 a Gambia, dubu 80 a Nijar, dubu 25 a Mali, dubu 80 Tanzania, dubu 120 Saliyo, dubu 53 a wasu sauran kasashen Afirka.

A shiri na biyu kuma za a buga dubu 760, Najeriya za ta samu dubu 80, Saliyo dubu 120, sai dubu 80 a Philipines.

3542078


captcha