IQNA

20:27 - November 06, 2016
Lambar Labari: 3480912
Bangaren kasa da kasa, an nada Sheikh Tahir Muhammad a matsayinsabon wakilin cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci ta duniya.
An Nada Sabon Wakilin Cibiyar Kusanto Da Mazhabobin Muslunci Ta Duniya A Ethiopia
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, sheikh Tahir Muhammad wanda fitaccen malamin jami'a ne a kasar, ya gana da shugaban karamin ofishin jakadancin Iran Sayyid Hassan Haidari a yau.

A yayin ganawar tasu an tabbatar masa da matsayin wakilin babbar cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci ta duniya a kasar Ethiopia.

Karamin jakadan kasar ta Iran kuma shugaban ofishin yada al'adun musluncia Ethiopia ya bayyana cewa, bisa la'akari da babban rashin da aka yi na sheikh Kamil Abubakar Sharif, wanda shi ne wakilin cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci a Ethiopia, a maye gurbinsa da sheikh Tahir Muhammad.

Ya kara da cewa, bisa la'akari da irin gagarumar rawar da wannan babban masani yake takawa a fagage daban-daban na ilimi da fadakarwa atsakanin musulmi, da kuma yadda yake kokarin isar da sakon musulunci a kasar, a kan haka aka zabe shi, kuma ko shakka babu zai iya ci gaba da gudanar da ayyukan da marigayin yake yi a lokacin rayuwarsa.

Kasar Ethiopia wadda akasarin mutanen da ke zaune a cikinta mabiya addinin kirista ne, na daya daga cikin cikin kasashen da ake samun kyakkyawar alaka da dangantaka a tsakanin msuulmi da kirista a kasar, inda a lokuta da dama kiristoci sukan haarci tarukan musulmi, kamar yadda musulmi ma sukan halarci tarukan kiristoci, saboda hadin kai da zaman lafiya,a daidai lokacin da kowannensu yake rike da addininsa da akidarsa.

3543721


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: