IQNA

18:48 - November 10, 2016
Lambar Labari: 3480925
Bangaren kasa da kasa, masu kula da shafin yanar gizo na Donald Trump zabebben shugaban kasar Amurka sun cire irin kalaman batuncin da ya rika yi a kan musulmi daga shafin nasa.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na express cewa, baya ga cire kalaman batunci kan musulmi daga shafin Trump, a lokacin jawabinsa na farko bayan samun nasara, ya bayyana cewa za su yi aiki tare da kowa ba tare da nuna kyama ga wani ba.

Donald Trump ya kara da cewa, duk da cewa maslahar Amurka ita ce a gaba a kan komai a wurinsa, amma kuma zai yi mu'amala tare da dukkanin kasashe na duniya bisa mutunci da girmama juna.

Kamar yadda ya ce kuma zai hada da kai tare da dukkanin mutanen Amurka ba tare da nuna banbanci na addini ko siyasa ko kabilanci ba, sabanin kalaman da aka saba ji daga bakinsa a lokutan baya.

A cikin watan Disamban shekarar 2015 da ta gabata ce, Trump ya bukaci da a hana musulmi shiga cikin kasar Amurka, tare da yin kira da a rika sanya ido a kan sauran musulmin da ke cikin kasar, tare da bincika masallatansu da wuraren ibadarsu.

3544898


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: