Bayanin ya ce taron yana samun halartar masana daga dukkanin bangarori biyu na musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, musamman ma dai mabiya addinin kirista, wadanda suke da bukatar sani abu kan muslunci.
Babbar manufar taron dai wanda ba shi ne karo na farko ba, ita ce fito da hakikanin fuskar muslunci ga wadanda ba musulmi ba, domin kuwa bata sunan muslunci ya yi tasiri matuka musamman ma a cikin kasashen yammacin turai kan batun ta'addanci.
An gabatar da laccoci kan matsayin muslunci dangane da zamantakewa da kuma siyasa gami da akidar sauran addini da ma yadda muslunci yake kallon dan adam baki daya, wanda kaida a muslunci ita ce Allah ya aiko manzonsa mai tsira da amincin Alllah da iyalansa tasrakaka a matsayin rahma ne ga bil adama baki daya.
Su a nasu bangaren wadanda suka halarci taron daga bangaren mabiya wasu addinai sun gabatar da jawabansu da kuma yin tambayoyi kan abin da ya shige musu kan muslunci kuma an ba su amsoshi daidai da tambayoyin nasu.
Kiamnin shekaru 7 kenan ana gudanar da wannan taro wanda yake a kowace shekara yake kara bunkasa.