IQNA

23:41 - November 13, 2016
Lambar Labari: 3480937
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taron kawara juna sani kan ma’anar kyamar musulunci wanda zai gudana a birnin Alkahira na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bawwaba News cewa, a ranar talata mai zuwa za a gudanar da taron a cibiyar Guarden City da ke Alkahira tare da halartar masani dan kasar Faransa Lora Jeric.

Bayanin ya ce wannan zaman taron dai babbar manufarsa ita ce kara fito da ma’anar musulunci sabanin yadda ake tallata shia tsakanin wasu kasashe musamman ma na yammacin turai, wadanda suke da karancin masaniya dangane da wannan addini mai girma.

Zaa gudanar da laccoci kan muslunci da kuma Kalmar kyamar musulunci wadda ta yi ta yaduwa a shekarun baya-bayan nan a cikin kasashen turai, domin tabbatar da kuren masu akidar kymar musulunci, tare da fitar da bayanai kan ainahin koyarwar musulunci ta gaskiya, wadda ta ginu a kan girmama dan adama da sauran addinai.

Lora Jeric daya ne daga cikin masana daga kasar Faransa wanda shi ma zai halarci taron kuma zai gabatar da lacca, musamman ma ganin cewa yana da masaniya kan muslunci, inda yake iyakacin kokarinsa domin wayar da kan mutane a kasashen turai kan cewa muslnci ba addinin ta’addanci ba ne kamar yadda suka dauka.

Wannan cibiya da zata dauki nauyin taron an kafa ta ne tuna cikin shekara ta 2013, kuma tana da rassa daban-daban a kasashen larabawa, amma babbar cibiyarta tana kasar Morocco.

3545492


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: