IQNA

An Samu Karuwar Hare-Haren Masu Kyamar Musulmi Kan Masallatai A Birtaniya

22:53 - November 22, 2016
Lambar Labari: 3480964
Bangaren kasa da kasa, wata cibiya mai zaman kanta ta ce an samu karuwar hare-haren da masu tsananin kyamar muslunci suke kaddamarwa kan masallatai da cibiyoyin musulmi a kasar Birtaniya a inda aka kai hari kan masallatai fiye da 100.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin shafaqna da ya habarta cewa, cibiyar Tell Mama ta kasar Birtaniya da ke sanya ido kan ayyukan kyamar musulmi kasar Birtaniya, ta fitar da rahoton da ke cewa hare-haren da ake kaiwa kan masallatan musulmi da cibiyoyinsu a birane daban-daban na kasar ya karu a cikin shekaru 4 da suka gabata, inda aka kai hari kan masallatai kimanin 100 a biranan kasar.

Wanann cibiya da ke gudanar da aikinta tare da taimakon gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa, ko shakka babu wannan ba ya rasa nasaba da kyamar musulunci da ke karuwa a kasashen nahiyar turai sakamakon ayyukan ta'addanci da wasu ke aikatawa da sunan muslunci, duk kuwa da cewa wannan ba zai taba zama hujjar kai hari kan sauran musulmi da ba su ji ba su gani ba.

Daga cikin abubuwan da masu kyamar musulunci ke yi a Birtaniya har da kona masallatai da cibiyoyin musulmi, da kuma yin rubuce-rubuce na batunci akan bangayen masallatai da wurarren tarukan addini.

3548099


captcha