Bangaren kasa da kasa, wata mata musulma 'yar kasar Azarbaijan, ta rubuta cikakken kur'ani mai tsarki da hannunta a kan kyallayen alhariri.
Kmfanin
dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin yada
labarai na jaridar daily Sabah cewa, Wata mata musulma mai suna Tunzal Muhammad
Zadah 'yar kasar Azarbaijan yar shekaru 33 da haihuwa,ta rubuta cikakken
kur'ani mai tsarki da hannunta a kan kyallayen alhariri, tare da yin amfani da
tawada da aka hada ta da ruwan zinari da azurfa.
Bayanin
ya ci gaba da cewa yana daga cikin ayyuka da aka gudanar masu daukar hankali
matuka da suka danganci kur’ania cikin
tarihi, kuma wannan kwafin kur’ani ya shiga cikin tarihi.
Wannan
mata dai ta dauki shekaru kimani uku a jere tana gudanar da wannan aiki mai
babbar kima, wanda kuma cikon ikon Allah ta samu nasarar kammala aikin a cikin
wannan shekara.
Da
dama daga cikin masana sun nuna mamakinsu matuka dangane da yadda wannan mata
ta gudsanar da wannan gagarumin aiki a cikin kankanin lokaci.
354816